Nijar:Yunkurin magance matsalar bakin haure
July 27, 2017
A Jamhuriyar Nijar majalisar dokokin kasar ce ta tashi haikan don tabbatar da shirin dakile matsalar kwararar bakin haure inda ta umarci wasu 'yan majalisar kasar da su soma shirya taro da gangami don wayar da kawunan al'umma a duk yankunan kasar da zummar cimma wannan manufa, Ko baya ga gangamin da 'yan majalisar ke yi don samun hadin kan jama'a wajen kawar da matsalar, 'yan majalisar dokokin sun kuma yarda da dokar nan da suka jefa wa kuri'a a shekarar 2015 mai tabbatar da hukunci kan wadanda aka kama da laifin safarar bakin haure. Ba shakka kafa sansanonin da ke tarbar 'yan gudun hijira da ke kokarin tsallakawa zuwa kasashen Turai da gwamnatin Nijar ta samar, hadin gwiwa da jama'a da kuma Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa dubban matasa daga kasashen yammacin Afirka daga kaurace wa wannan doguwar tafiyar marar tabbas.
Shigar majalisar dokokin Nijar wajen yaki da kwararar bakin haure na nuni da cewa majalisar ta shiga a dama da ita wajen kwatar wa jama'a haddinsu tare da kare talakawa da take wakilta a ko ina cikin fadin kasar. 'Yan majalisar dokokin na shirya gangami ne da tattaunawa ta zahiri tsakaninsu da al'umma musamman ma a yankunan da matsalar ta kwararar bakin haure da 'yan ci- rani ke da kamari kamar Agadez da Tahoua da yankin Zinder. Matsalar na daukar wani sabon salo abin da ya sa majalisar take fatan samun hadin kai daga jama'a don a gudu tare a tsira tare.
To kowane tasiri wannan sabon tsarin na majalisar dokoki zai yi
Honorable Hamma Assa dan majalisar dokoki mai irin wannan fafutuka, ya ce nasarar da ake son cimma ita ce ta shawo kan shugabannin kasar saboda matsalar babba ce ba ma ga kasar Nijar kadai ba har ma da sauran kasashen Afirka, ganin bakin hauren na tasowa ne daga wasu kasashen Afirika su kuma yada zango a birnin Yamai kafin su tashi zuwa Agadez, daga nan ne suke watsuwa su bi ta Tamarasset wasu kuma su bi ta Libiya ta hanyar Sahara.
'Yan majalisar da kansu sun nuna cewar sun kwana da sanin cewar tilas sai kasashen da kansu su tashi haikan wajen magance matsalolin da ke addabar matasa ta rashin aikin yi da zaman kashe wando da ke kara harzuka jama'ar daukar matakin na yin wannan dogon balaguro. Saboda haka duk wani amfani da karfi a yanzu ba zai iya magance bala'in ba inji Hama Assa dan majalisar na dokoki.