Nijar za ta iya dakile takunkumin ECOWAS
August 14, 2023Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine ya shaida wa tashar Deutsche cewa ko dayake kalubale ne wanda babu adalci a cikinsa kakaba musu takunkumi, amma za su iya shawo kansa.
Kungiyar raya ci gaban tattalin arzikin kasashen Afrika ta yamma ECOWAS ta sanya wa Nijar takunkumi bayan juyin mulki kuma ba ta fidda yiwuwar amfani da karfi a kan sojojin da suka kifar da gwamnatin zababben shugaba na dimukuradiyya Bazoum Mohammed ba
Kasashen kungiyar sun katse harkokin kudade da wutar lantarki da kuma rufe iyakokinsu da NIjar.
Tun da farko sojojin sun ce takunkumin ya kuntata wa jama'a ta hanyar rashin samun magani da abinci da wutar lantarki inda suka baiyana matakin da cewa haramtacce ne na rashin imani da kuma rashin tausayin al'umma.
Sai dai Zein ya baiyana kwarin gwiwa da ziyarar tawagar Najeriya inda ya kara jaddada muhimmancin dangantaka tsakanin Nijar da Najeriya da sauran kasashen yammacin Afirka.
Ya kuma bukaci jama'a su nuna amincewa da sabbin mahukuntan kasar ta Nijar