Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisu
December 27, 2020Sama da mutane miliyan bakwai ne suka yi rijistar zabe a kasar. 'Yan takarar shugabancin kasar 30 ne ke kokarin karbar mulki daga hannun shugaba mai barin gado Muhammadou Issoufou wanda ya zamo shugaban kasa a shekarar 2011, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2010.
Ana ganin koma wa ye ya yi nasarar lashe zaben na yau zai fuskanci manyan kalubale da suka hada da matsalar tsaro da na cin hanci da rashawa. Can a dayan hannun kuwa a jamhuriyar Afirka ta tsakiya, su ma a yau ne a su ke gudanar da manyan zabuka na shugaban kasa da na 'yan majalisu duk kuwa da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta a halin da ake ciki.
Za a fafata zaben na yau ne tsakanin shugaba Faustin-Archange Touadera da wasu mutum 17. Ofishin kare hakkin bil'adama na MDD duniya ya yi gargadin hare-haren kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai ka iya kawo cikas a zabukan da ma rayukan alumma fararen hula.
Ko a Jumma'ar da ta gabata jami'an wanzan da zaman lafiya na majalisa mutum uku ne suka rasa rayukansu sakamakon wani hari da wata kungiya ta kai. A cewar MDD 'yan tawayen na samun goyon bayan tsohon shugaban kasar ne Francois Bozize