An kama wani dan Libiya mai sarafar baki
December 30, 2022An kama mutumin ne bayan wani bincike na hadin gwiwa tsakanin 'yan sandan Nijar da Faransa da Spain kamar yadda wata majiyar 'yan sandan Faransa ta bayyana. Wanda ake zargin,wanda aka kama a ranar 20 ga watan Disamba a Agadez, a arewacin Nijar,ya ba da tabbaci a lokacin sauraren karar da masu binciken suka yi masa cewa, ya rika aika ‘yan ci-rani sittin a mako har tsawon shekaru bakwai. Galibinsu daga kasashen yankin yammacin Afirka da tsakiya, wadanda da farko ake kai su Nijar cikin motocin daukar kaya, tare da kaucewa manyan birane. Daga nan a wuce da su zuwa Libiya ko Aljeriya, kafin a tsalaka da su zuwaTurai. Arewacin hamadar Nijar ya yi kaurin suna wajen safarar bakin haure da muggan kwayoyi da makamai sannan kuma yana tattare da kungiyoyin masu jihadi.