Obama-Ba zaman lafiya muddin masu kudi na danne talakawa
September 20, 2016
Shugaba Barack Obama na Amirka ya bayyana kalamai masu zafi a lokacin da yake jawabinsa da ke zama na karshe a matsayin shugaban Amirka gaban taron koli na Majalisar Dinkin Duniya inda ya yi suka mai zafi ga kasar Rasha da ke mara baya ga mahunkuntan Siriya da shirin tsagaita wutarsu ya rushe da ma katsalandan din mahukuntan na birnin Moscow a Ukraine.
Shugaba Obama ya dai jaddada cewa samar da waraka a rikicin na Siriya mai yiwuwa ne kawai idan aka bi hanyoyi na diplomasiya.
Ya kuma juya kan batun zaman takewa a duniya inda ya nunar da cewa zaman lafiya a duniya ya dogara a kokari na rage wagegen gibi da ke tsakanin talakawa da masu hannu da shuni:
"Duniyar da ta kasance kashi daya cikin dari suke rike da arzikin al'umma ragowar kashi 99 ko oho ba za samu daidaito ba."