Obama ya aike da saƙo ga al'ummar Iran
March 20, 2009Babbar alamar dake nuna cewa, Obama da gaske yake yi, wajen dawo da kyautatuwar mu'amala tsakanin ƙasar Amirka da Jamhuriyar Musulunci ta Iran, shi ne wani kaset ɗin bidiyo mai ƙunshe da jawabai, da Obaman ya aikawa shugabanni da kuma ilahirin al'ummar Iran. An daidaici lokacin da al'ummar Iran suke fara bikin sabuwar shekararsu ta Nowruz, sannan aka aika da wannan saƙo na Obama. Inda a cikin kaset ɗin Obama ya bayyana cewa, Amirka a shirye take ta dawo da kyautatuwar mu'amala da Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Obama ya buɗe kaset ɗin bidiyon ne yana mai cewa;
"Ya ce, a yau ina son na miƙa saƙon fatan alheri ga ɗaukacin al'ummar da suke bikin shekarar Nowruz a faɗin wannan duniya. Wannan biki ne mai daɗɗaɗen tarihi kuma na tuna baya domin a gyara gaba, ina fata za ku ji daɗin gudanar da wannan biki, tare da 'yan'uwa da abokan arziki''
Obaman ya ci gaba da cewa, gwamanatinsa a shirye take ta bi sahun lalama a matsayin hanyar da za ta warware duk wata tsamin dangantaka tsakaninta da Iran. A ɗaya hannun kuma yana mai kira ga Iran ɗin da ita ma ta ɗauki ingantattun matakai wajen kyautata dangantakarta da Amirka da ma sauran ƙasashen duniya.
Da ya juya kan shugabannin Iran ɗin Obama ya yi kira a gare su da cewa;
"Ina so na fito ƙarara na bayyanawa shugabannin Iran cewa, mun sami saɓani da yawan gaske da suka daɗe suna faruwa a tsakaninmu. Gwamnatina yanzu ta shirya domin ta bi hanyoyin diplomasiyya yadda za a tattauna jerin batutuwan da muke da saɓani akai, a kuma lalubo bakin zaren warware su, domin a ci gaba da kyakkyawar mu'amala tsakanin Amirka da Iran da ma sauran ƙasashen duniya."
A ƙarshen jawabin nasa, Obama ya yi wani hannunka mai sanda yana mai cewa;
"Na san cewa wannan buri ba zai samu ba cikin sauƙi. Domin akwai waɗanda suka dage lallai sai dai mu ci gaba da zama cikin waɗannan banbance-banbance dake tsakaninmu. Amma ina mai kira a garemu da mu tuna waƙar nan da mawaƙin nan na Iran Sa'adi ya rubuta, inda ya ce, ''Dukkaninmu 'ya'yan Adam ne, kuma an haliccemu ne akan manufa guda''.
A nata ɓangaren Hukumar Jamhuriyar Musulunci ta Iran, ta bakin mai baiwa shugaban ƙasa shawara akan harkar jarida Ali Akbar, ta yi maraba da wannan saƙo da Obama ya aika mata, kuma ta yi kira ga Shugaban na Amirka da ya ƙarawa daɓensa makuba, ta hanyar aiwatar da wannan saƙo a aikace, tare da gyara kurakuran da aka tafka a baya.
Shi ma shugaban Tarayyar Turai Javier Solana ya yi fatan sabon shafin da Obaman ya buɗe da Iran, zai haifar da ɗa mai idanu.
Fadar ta White House ta bayyana cewa, za a samar da kwafen wannan bidiyon na jawabin Obama a cikin harshen Farisanci, a kuma rarraba su ga kafafen yaɗa labarai dake yankin.
Mawallafi: Abba Bashir
Edita: Hauwa Abubakar Ajeje