Barack Obama ya yi jinjina ga manufofin Marigayi Mandela
July 17, 2018Tsohon Shugaba Barack Obama na Amirka ya yi jawabin jinjina ga manufofin Marigayi Nelson Mandela tsohon shugaban Afirka ta Kudu wanda ya jagoranci gwagwarmayar kawo karshen mulkin nuna wariyar launin fata. Haka na zuwa albarkacin cika shekaru 100 da ake yi a wannan Laraba da ke zama 18 ga watan Yuli na lokacin da aka haifi Marigayi Mandela.
Wannan ke zama jawabin Obama tsohon shugaban Amirka mafi jan hankali tun lokacin da ya ajiye madafun iko a farkon shekarar da ta gabata ta 2017. Shi dai Marigayi Mandela da ke cika shekaru 100 da haihuwa ya kwashe tsawon shekaru 27 a gidan fursuna saboda nuna adawa da tsarin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu, bayan an sake shi a shekarar 1990 daga bisani ya zama shugaban kasa a shekarar 1994 wanda kuma ya tabbatar da ganin hadin kai tsakanin mutanen kasar ta Afirka ta Kudu.
Lokacin jawabin tsohon shugaban na Amirka Obama ya nuna takaicin bisa samun tasirin masu siyasa da nuna banbanci yanzu haka.