Obama ya yi bankwana da shugabannin kasashen Turai
November 18, 2016A cewar fadar shugaban kasar na Amirka mai barin gado, shugabannin sun amince da dukannin huldodi na soja har da na kungiyar tsaro ta NATO, sannan kuma sun ce za a ci gaba da kakabawa Rasha takunkumi har sai an aiwatar da gaba dayan yarjejeniyar da aka cimma ta birnin Minsk. Sai dai sabon shugaban kasar ta Amirka Donald Trump a lokacin yakin neman zabensa, ya soki wadannan batutuwa guda biyu inda ya ce zai kawo gyara a kan su.
Shugaba Obama dai ya yi bankwana a wannan Juma'a ga sauran shugabannin Turai da suka hada da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da Theresa May ta Britaniya da Mariano Rajoy na Spain da Matteo Renzi na Italiya da kuma Shugaba François Hollande na Faransa, kafin daga bisani ya tashi zuwa kasar Peru inda zai halarci taron huldar tattalin arziki na kasashen (APEC) na Asiya da Passifique.