1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya yi fatan Trump zai iya fuskantar Rasha

November 17, 2016

Shugaba Barack Obama ya yi wannan furucin ne bayan ganawarsa da Angela Merkel wadda ta yabwa dangantakar Amurka da Tarayyar Turai da kuma Jamus.

https://p.dw.com/p/2SrNV
Deutschland | US-Präsident Obama wird von Bundeskanzlerin Merkel in Empfang genommen
Hoto: Reuters/F. Bensch

Shugabar gwamnatin Jamus ta yabawa kyakkyawar dangantakar aiki tsakanin Amurka da Kungiyar Tarayyar Turai cikin shekaru 8 na gwamnatin Barack Obama. A taron manema labaru na hadin gwiwa da suka gudanar da yammacin wannan Alhamis a birnin Berlin, shugabannin biyu sun yi fatan cewar, wannan dangantaka za ta dore a sabuwar gwamnatin Donald Trump mai jiran gado.

" A yau bazan ce mun kai ba, sai dai mun kusan kai karshen kyakkyawar dangantaka ta shekaru takwas, wanda daga bangarena zan iya cewar, alakar Amurka da Jamus da kuma Turai da Amurka sun ta'allaka ne kan manufofinmu na ketare. Wanda a hannu guda ya danganta da muradu, kana a daya bangaren kan manufofinmu".

Shugabar gwamnatin Jamus din ta ce manufofinsu duka daya ne na tabbatar da tafarkin demokradiyaya da 'yan cin walwala da kare hakkin bil'adama, da muradun cimma sassaucin ra'ayi. A yayin da Merkel ke godewa shugaban Amurkan mai barin gado, ta yi alkawarin aiki tare da sabon zababben shugaba.

A nashi bangare Obama ya yi fatan cewar, Donald Trump zai iya fuskanatar Rasha idan bukatar hakan ta taso, tare da sanin yadda zai yi kyakkyawar alaka da Moscow wurin da akwai bukatar hakan. Ya ce a wani mataki na magance wasu manyan matsaloli da duniya ke fuskanta, ya zamanto wajibi mu yi aiki tare da Rasha.