1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama ya yi kashedi ga ƙasar Iran

March 3, 2012

Obama yace Amirka ba ta fidda tsammanin yin amfani da matakin soji akan Iran ba matuƙar ta ci gaba da shirin ƙera makamin nukiliya.

https://p.dw.com/p/14EXV
President Barack Obama speaks at the James Lee Community Center in Falls Church, Va., Wednesday, Feb. 1, 2012. Obama outlined a proposal he proposed in his State of the Union address to allow homeowners with privately held mortgages to take advantage of record low rates, for an annual savings of about $3,000 for the average borrower. (Foto:Susan Walsh/AP/dapd)
Hoto: dapd

Shugaban Amirka Barack Obama ya yi kakkausar kashedi tare da barazanar ɗaukar matakin soji akan ƙasar Iran idan ta ci gaba da shirin ƙera makamin ƙare dangi. Kashedin ya zo ne 'yan kwanaki gabanin ziyarar da shugabannin Israilan za su kai zuwa Washington. A ranar Firaministan Israila Benjamin Netanyahu a lokacin da ya yada zango a ƙasar Kanada a kan hanyarsa ta zuwa Amirka ya yi gargaɗi bisa abin da ya kira 'yancin ɗaukar mataki idan aka la'akari da irin barazanar da Iran ta sha yi a baya. Netanyahu yace Israila na da damar ɗaukar zaɓin da ya dace akan ƙasar Iran wadda shugabanta Mahmoud Ahmedinejad ke da'awar haƙƙin wanzuwar Israila a doron ƙasa. Ita dai Iran ta sha nanata cewa shirinta na nukiliya na lumana ne domin samar da wutar lantarki ga jama'arta.

Mawallafi: Abdullahi Tanko Bala
Edita: Saleh Umar Saleh