1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obama zai yi jawabi a gaban 'yan majalisun Amirka

Salissou BoukariJanuary 12, 2016

A wani abun da ya zamanto al'ada ga kasar Amirka, a wannan Talata ce Shugaban kasar zai yi jawabi mai mahimmanci ga al'umma kafin tsunduma cikin yanayi na siyasa.

https://p.dw.com/p/1HbhH
Barack ObamaHoto: Getty Images/AFP/B. Smialowski

Ana sa ran shugaban zai isar da dumbun sakonni ga Amirkawa kafin shiga guguwar siyasa da kasar za ta yi nan gaba kadan, inda jam'iyyu za su fara tantance 'yan takararsu daga ranar daya ga watan Febrairu mai zuwa. Irin wannan jawabi dai ya zamanto na al'ada ga shugabannin Amirka, inda Obama shi ne shugaba na 44 wanda zai yi shi, wanda a cikinsa shugaban zai sanar da mahimman ayyukan da gwamnatinsa ta yi da kuma sabon hasashen mokamar kasar ta Amirka a bayan wannan shekara ta 2016.

Ana saran 'yan takara uku masu neman shugabancin kasar ta Amirka daga jam'iyyar Repulicain da ke da kujeru a majalisa za su halarci taron. Shugaba Obama dai zai tabo batun bunkasar tattalin arzikin kasar, da kuma irin gogormayar da ya sha tun bayan hawansa kan karagar mulki a shekara ta 2009.