1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Obasanjo ya ƙalubalanci Goodluck Jonathan

December 13, 2013

A cikin wata wasiƙar da tsohon shugaban Najeriyar ya aike da ita ga shugaba Jonothan ya zarge shi da rashin yin adalci da kuma gaza tabbatar da tsaro a ƙasar

https://p.dw.com/p/1AZ9z
Porträt - Olusegun Obasanjo
Hoto: Getty Images

Wasiƙar da tsohon shugaban Najeriyar Olusegun Obasanjo ya rubuta wa shugaba Goodluck Jonathan na ci gaba da haifar da cece-ku-ce na taƙaddama musamman saboda batutuwan da ta ƙunsa da tuni ta girgiza Najeriyar da ma tambayar makomar siyasar kasa.

Wasiƙar ta yi tsokaci a kan rashin tabbatar da gaskiyya da adalci ga shugaba

To wasikar ta Cif Obasanjo ga shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan na ci gaba da zama wacce ke ɗoyi tamkar ruɓaɓen ƙwai a ɗaukacin Tarayyar Najeriyar, domin kuwa ƙarara a fitli ba tare da shakka ko tsoro ba Obasanjo ya yi kashedi ga shugaban na Najeriya a kan yadda yake tafiyar da harakar mulkin ƙasar wanda ya ce akwai buƙatar gyara tun kafin a makara. Batutuwan da suka girgiza fadar shugaban Najeriyar musamman tonon silili da ya yi a kan batun rashin tsaro da ma ɗaukar wasu zarattan jami'an tsaron da ya ce shugaban ya yi, ya zuwa tuna ma shi cewar ya fa yi alaƙawarin zai yi wa'adi ɗaya ne a kan karagarar mulkin. Kuma kaucewa daga wannan matsayi na jefa Najeriyar ga komawa halin rashin tabbas da ta samu kanta a ciki a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriyar Janar Sani Abacha. Zafin da wasiƙar ta yi dai ya sanya tambayar shin wanne tasiri wanna wasiƙa ka Najeriyar? Tuni dai jam'iyyun adawa da ma ƙungiyoyin shioyoyin Najeriya ke matsain lamba ga shugaban na lallai sai ya ba da ammsa, a kan wannan wasiƙa don sanin matsayinsa da ma inda aka dosa. Alhaji Tijjani Musa Tumsa shi ne sakataren jam'iyyar adawa ta CPC ya ce akwai abin da wannan ke nuna a zahirance a kan halin da Najeriyar ta ke ciki.

Nigeria Tag der Demokratie
Hoto: DW/U. Musa

Fadar gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani ba har yanzu

Har zuwa wannan lokaci dai fadar ta gwamnatin Najeriyar da ake wa kalLon ba ta farfaɗo daga juyayin wannan wasiƙa ta Obasanjo ba, musamman yadda aka yi ta kai ga kafofin yaɗa labaru na ƙasar, domin shugaban Jonatha ɗin ya hana ɗaukacin jami'ansa maida martani, abin da ke ƙara jefa shakku da ma tabbabar inda aka dosa, amma ga Dr Abubakar Umar Kari na mai cewa fadar shugaban fa ba ta ga ta yin shiru a kan wannan batu ba. Cif Obasanjo dai ba baƙo ba ne wajen rubuta wasiƙu ga shugabanin Najeriya a kan abin da yake jin bai masa dai-dai ba, to sai dai sanin cewa shi ne musababin Shugaba Jonathan kai wa ga wannan muƙami, mutane da yawa na shakku shin ba ɓatawar da ake hangen sun yi ba ne ya sanya shi wannan ɓaɓatu, ko kuwa ƙoƙarin wanke kai ne daga hali na rashin tabbas da ake ganin makomar Najeriya ta kama hanyar shiga.

Goodluck Jonathan Präsident Nigeria Fernsehansprache ARCHIV
Hoto: Pius Utomi Ekpei/AFP/Getty Images

Daga ƙasa za a iya sauraron wannan rahoto haɗe da rahoton da wakilinmu na Bauchi ya aiko mana a kan batun haɗe da rahoton da wakilinmu na Abuja Uwais Abubakar Idris ya aiko mana, da kuma hira da Saleh Umar Saleh yayi da Dokto Aliyu Tilde mai nazari a kan al'amura a Najeriya

Mawallafi : Uwais Abubakar Idris
Edita : Abdourahamane Hassane

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani