Scholz na Jamus na ziyara a Turkiyya kan Gabas ta Tsakiya
October 19, 2024A Asabar din nan ce shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ke fara wata ziyarar aiki a birnin Santanbul na kasar Turkiyya, inda zai gana da shugaba Recep Tayyip Erdogan kan wasu muhimman batutuwa.
Daga cikin batutuwan da shugabannin biyu za su tattauna a kai, sun hada da rikicin Gabas ta Tsakiya da matsalar kwararar bakin haure masu shiga Turai, sai kuma harkokin tsaro da na tattalin arziki, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Jamus DPA ya rawaito.
Karin bayani:Shugaba Erdogan na ziyara a Jamus
Jamus dai na neman hadin kan Turkiyya, don korar bakin hauren da suka shiga kasar ta barauniyar hanya, bayan cimma wannan yarjejeniya da kasashen biyu suka yi a baya bayan nan.
Karin bayani:Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai gana da shugaban Amurka Joe Biden kan Ukraine da Gaza
Haka zalika batun yakin Ukraine na daga cikin al'amuran da za su yi duba a kai, a yayin ziyarar ta Mr Scholz a Turkiyya.