An yi amfani da guba a Siriya
June 13, 2018Talla
Hukumar ta ci gaba da cewa an yi anfani da Sarin a birnin Ltamenah a yankin Hama a ranar ashirin da hudu da ashirin da biyar na watan Maris a shekarar 2017 a yankin na Hama da ke kudancin kasar. An tabbatar da hakan ne bayan binciken hukumar.
Wadannan sinadaran na daga cikin wadanda aka haramta yin anfani da su ko da a lokacin rigingimu ne. An zargi bangaren gwamnatin Bashar al-Assad da laifin yin anfani da makaman masu guba a kan al'umma a yankin da a wancan lokacin ke karkashin ikon 'yan tawaye, lamarin ya janyo asarar rayukan mutane barkatai.