OPCW ta kammala bincikenta a Siriya
May 4, 2018Tawagar ta koma ofishinta da ke kasar Holland inda daga nan ne za ta shirya rahoto kan sakamakon binciken. Kungiyar ba ta da ikon fadin sakamakon binciken na ta.
Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bakin mai magana da yawunta Maria Zakharova ce ta sanar da hakan. A ranar bakwai ga watan Afrilun aka kai hari da makami mai guban a garin na Douma da a wancan lokacin ke karakashin ikon 'yan tawaye, kasashen yamma sun zargi dakarun Rasha da na gwamnatin Siriya da laifin anfani da makamin da dokar kasa da kasa ta haramta akan farraren hula.
An kuma zargi kasashen biyu da yunkurin hana tawagar masana masu aikin binciken shiga yankin na Douma bayan faruwar lamarin, an shirya daukar matakin aza takunkumi kan wadanda aka samu da laifin hannu a al'amarin da ya salwantar da rayukan mutane kusan dari ciki har da yara kanana.