1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Oscibi Johann dan fafatukar neman 'yancin jama'a

Eunice Wanjiru/ KSSeptember 30, 2015

Kungiyar kare hakin jama'a ta "Balai Citoyen" ta taka rawa a boren da aka yi a Burkina Faso cikin watan Oktoban 2014. Oscibi Johann da makadansa na zama alamar wata yekuwar 'yanci na matasan kasar.

https://p.dw.com/p/1GfuP
Burkina Faso Oscibi Johann von Balai Citoyen
Hoto: DW/G. Vollmer

Oscibi Johann da sauran makada kusoshi a cikin kungiyar ta matasa suna hadin kai da sauran kungiyoyi masu fafatuka a Afirka.

Tashar rediyon Horizon FM a birnin Ouagadougou na zama wani dandali ga Oscibi Johann, dan fafutukar neman 'yanci kuma mawakin kidan Reggae, wajen fadin albarkacin bakinsa.

“Ina amfani da wannan shiri ina aike wa da sako ga jama'a. A nan ina samun sukunin bayyana ra'ayi na. A gare ni rediyo murya ce ta 'yanci.”

Oscibi ya zama mai bayyana 'yancinsa a Burkina Faso. A farkon shekara hukumar leken asirin kasar Kwango ta jefa su kurkuku a Kinshasa, bayan sun yi jawabi a wani taron masu fafatukar neman 'yanci a kasar ta Kwango.

Yanzu mawakan daga kasashe makwabta na zama wani fata ga matasa a wurare daban-daban a nahiyar Afirka.

“Mun hadu a wani otel a Kwango, an gaiyace mu babban taro kan 'yancin jama'a. Na yi matukar farin cikin saduwa da takwarorina 'yan fafatuka. Tare da su muka gabatar da wasan kade-kade a wajen babban taron, tare da su kuma muka zauna kurkuku. Yanzu wannan ne karon farko da muka sake haduwa.”

Taron kungiyar jama'a a wajen birnin Ouagadougou

Oscibi Johann ya gaiyaci masu fafatuka na kasar Senegal wajen taron. Shigar da bakin na kasa da kasa kuwa ya zama wata karramawa ga mambobin kungiyar jama'ar unguwar, ba su kuma bata lokaci ba wajen rera takensu.

Kongo Le balai Citoyen-Aktivist Oscibi Johann
Masu fafatuka na kungiyar Balai Citoyen a gun wani taron manema labarai a birnin KinshasaHoto: Getty Images/AFP/F. Scoppa

Fadel Barro na Kungiyar Y en a Marre daga kasar Senegal ya yi jawabi yana mai cewa:

"Mun kawar da akidar bauta. 'Yan nahiyar Afirka sun kawo karshen zamanin mulkin mallaka. Saboda haka a gani na abu ne mai yiwuwa mu katse hanzarin shugabannin kasashe da ke son zama kan mulki har abada.”

Neman 'yanci da tsabtace muhalli

Wannan dai shi ne burin kungiyar jama'a ta “Balai Citoyen”. Mambobinta sun kwashe yini guda suna kwasan shara a unguwar Karpala. A cikin harshensu wato Mooré, sun yi wa matan kasuwa bayani cewar bai kamata a yi ta zubar da shara barkatai a ko-ina ba.

Daga baya an duba sautin wakoki gabanin wani wasan kade-kade na sada zumunta da aka yi kyauta ga mambobi da masu goya musu bayan a wani filin Allah ta'ala. Oscibi Johann ya yi karin haske.

“Wannan wasan kida ne na 'yanci. An gaiya ce ni in yi wakar 'yanci, demokradiyya da 'yancin dan Adam, domin shi ne manufarmu.”

Filin wasan ya kasance babban fage ga Oscibi Johann da mawakansa. Matasan masu fafatuka sun kuma yi amfani da wasan wajen yada sakonsu na siyasa ga sauran kasashe a nahiyar Afrika.