Sojojin hadin gwiwa sun kashe mayaka 100
December 10, 2021Talla
Akalla sojoji 13 ne aka kashe wasu bakwai sun ji rauni a cewar sanarwar sojojin hadin gwiwar kasahen biyu, wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka shafe makonni ana zanga-zangar kin jinin gwamnatin Burkina Faso kan rashin tsaro, matakin da ya kai ga shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore ya soke majalisar ministocinsa, yayin da Firaiministan kasar ya yi murabus.
Hare-haren masu jihadi a Burkina Faso a wannan shekara sun yi sanadiyar mutuwar dubban farafen hula, sama da mutane miliyan 1 da sun bar muhallansu, ciki har da wani mumunar hari a watan jiya da ya kashe jami'an tsaro da jandarmomi sama da 50.