?oƙarin Eu na kawo ƙarshen rikicin Nukiliyar Iran
November 22, 2007Talla
Wakilin Iran game da tattaunawar Nukiliya, Mr Saeed Jalili ya ce a ƙarshen watannan ne yake sa ran tattaunawa da kantoman Ƙungiyyar Tarayyar Turai, Mr Javier Solana.Tattaunawar a cewar rahotanni za ta kasance irinta ta farko ne, a ƙoƙarin da ake na samo bakin zaren warware rikicin Nukiliyar ta Iran. Bayan tattaunawar, Javier Solana zai yiwa Majalisar Ɗinkin Duniya bayanin yadda tattaunawar ta kasance. Hakan a cewar bayanai ka iya taimakon Majalisar gane inda aka kwana, a game da aniyar Iran ɗin na mallakar makamin na Atom. Ba sau ɗaya ba sau biyu ba, Iran ta dage kan cewa shirin ta na inganta rayuwar ´ Yan ƙasar ne, saɓanin zargin da ake na cewa shirin ka iya zamowa barazana ga Duniya.