1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan: An tarwatsa masu zanga-zanga

November 25, 2017

Jami'an tsaron kasar Pakistan sun yi amfani da karfi a wannan Asabar din wajen tarwatsa daruruwan masu zanga-zanga da suka toshe wani gwadabe da ke shigowa a Islamabad kusan makonni uku.

https://p.dw.com/p/2oFBm
Pakistan Islamabad Polizei Islamisten Sit-in
Hoto: AP Photo/A. Naveed

Masu zanga-zangar dai na bukatar ministan shari'ar kasar ya yi murabus sakamakon daukar wata doka da suka ce ta saba wa Muslunci. A cewar wani jami'in ofishin ministan cikin gida na kasar ta Pakistan, gwamnati ta tura 'yan sanda da sauran jami'an tsaro kimanin 8.500 domin gudanar da wannan aiki, inda suka yi ta harba barkonon tsohuwa, tare da harsasan roba akan masu zanga-zangar wadanda su kuma suka mayar da martani da jifa da duwatsu.

Tun daga ranar shida ga wannan watan na Nuwamba ne dai masu zanga-zangar akalla 2000 suka toshe gwadaben da ke tsakanin birnin na Islamabad da birnin Rawalpindi mai makwabtaka da shi lamarin da ya haddasa tarin matsaloli na zirga-zirga.