1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ba ta kare haƙƙin 'ya'yanta.

June 10, 2010

Amnesty International ta soki Pakistan bisa rashin kare haƙƙin 'ya'yanta.

https://p.dw.com/p/Nn7f
'Yan sanda ɗauke da gawar mayaƙin Taliban.Hoto: AP

Ƙungiyar kare haƙƙin bil Adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da abin da ta kira matakin kama karya na 'yan Taliban da ke tsunduma al'uma cikin halin ni 'yasu a yankin arewa maso yammacin Pakistan. A cikin rahoton da ta fitar a baya-bayan nan Amnesty International ta kira matakin da Taliban ke ɗauka tamkar mataki yin kisa, barazana da kuma gallazawa. Rahoton ya ci gaba da cewa waɗanda hakan ya fi shafa mata ne. Amnetsty ta kuma yi suka ga gwamnatin Pakistan game da nuna halin ko-in-kula akan halin da 'ya'yanta ke tsintar kansu a ciki. A ma jiya Laraba sai da 'yan Taliban suka kashe wani yaro mai shekara bakwai da haifuwa ta hanyar rataye shi saboda wai ya leƙa asirinsu.

Mawallafiya: Halima Abbas

Edita: Muhammad Nasiru Awal.