1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pakistan ta buɗe kan iyakar ta da Afganistan

July 4, 2012

NATO za ta samu damar isar da kayan abincin ga jami'an ta da ke a Afganistan, bayan amincewar da pakistan ta yi na sake sakin hanyoyin

https://p.dw.com/p/15Qso
epa03276843 Raja Pervez Asharf, who has been nominated as one of the leading candidates for Prime Ministership by President Asif Ali Zardari, leaves after a meeting with Chaudhry Shujaat Hussain (not in picture) head of coalition party Pakistan Muslim League Quaid (PML-Q) in Islamabad, Pakistan, 21 June 2012. The party and its coalition allies hold a comfortable majority in parliament, making Ashraf the likely winner among the five registered candidates in the National Assembly's vote scheduled for later Friday. The new Prime Minister will replace ousted Yousuf Raza Gilani, disqualified by a conviction for contempt of court. EPA/T. MUGHAL
Raja Pervez Ashraf fraministan PakistanHoto: picture alliance/dpa

Humomkin Pakistan sun tabbatar da shawara da suka yanke ta sake buɗe  kan iyakar su da ƙasar Afganistan,wacce ke zaman hanyar, kai kayan abincin ga jami'an rundunar tsaro ta NATO da ke a ƙasar.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton wacce ta tattauna da ministan harkokin waje na ƙasar ta ce sun amince su buɗe iyakar ba tare da wani sharaɗi ba na biyan diya.

Pakistan ɗin  ta rufe kan iyar ta ne da Afganistan  , tun a cikin watan Nuwanba da ya gabata  bayan wani harin bama bamai,

kan kuskure da rundunar tsaro ta ISAF  ta kai akan iyaka da Afganistan inda suka  kashe sojojin Pakistan guda 24.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane

Edita        : Umaru Aliyu