Pakistan ta buɗe kan iyakar ta da Afganistan
July 4, 2012Talla
Humomkin Pakistan sun tabbatar da shawara da suka yanke ta sake buɗe kan iyakar su da ƙasar Afganistan,wacce ke zaman hanyar, kai kayan abincin ga jami'an rundunar tsaro ta NATO da ke a ƙasar.
Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hilary Clinton wacce ta tattauna da ministan harkokin waje na ƙasar ta ce sun amince su buɗe iyakar ba tare da wani sharaɗi ba na biyan diya.
Pakistan ɗin ta rufe kan iyar ta ne da Afganistan , tun a cikin watan Nuwanba da ya gabata bayan wani harin bama bamai,
kan kuskure da rundunar tsaro ta ISAF ta kai akan iyaka da Afganistan inda suka kashe sojojin Pakistan guda 24.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu