1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Pakistan ta kai hari kan maboyar 'yan ta'adda a Iran

Binta Aliyu Zurmi
January 18, 2024

Sojin saman Pakisatan sun kaddamar da hare-haren ramuwar gayya a kan maboyar masu tayar da kayar bayan kasar da suka kafa sansani a Iran.

https://p.dw.com/p/4bQM6
Pakistan greift Ziele im Iran an
Hoto: Tasnim

A cewar ma'aikatar harkokin wajen Pakistan, kaddamar da farmakin da suka kai ya biyo bayan harin Iran da ya yi sanadiyyar mutuwar wasu kananan yara biyu a yammacin lardin Baluchistan.

Kafar yada labaran Iran ta rawaito cewa ta ji karar fashe-fashen bama-bamai  a yankin birnin Saravan da ke kan iyakar Iran da Pakistan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran IRNA ya ambato mataimakin gwamnan lardin Baluchistan, Ali Reza Marhamati, ke cewa su na ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

To da yake baya ba ta da kadan, kafar yada labaran Iran ta ce harin na Pakistan ya kashe akalla mata uku da yara hudu a yankin kudu maso yammacin Iran.