Pakistan ta saki wani jagoran Al-Qaida
September 21, 2013Tun da farko Ma'aikatar harkokin wajen Pakistan ta yi shelar sakin tsohon mataimakin ƙungiyar na Al-Qaida da ke Afghanisatan.
Wata sanarwar da ma'aikatar ta fidda ta ce gwamnatin Pakistan ɗin ta yanke hukuncin sakin Mullah Baradar ɗin ne domin tana ganin hakan zai taimaka wajen samun nasarar shirin sulhun da ake yi da 'yan kungiyar ta Al-Qaida a Afghanistan. Duba da matsayi da ya ke da shi da kuma irin kusancinsa da Mullah Muhammad Omar wanda 'yan ƙungiyar ke bai wa girma sosai. Gwamnatin Afganistan ta bakin wani kakakinta Aimal Faizi ta yi marhabin da sakin.
A baya dai Amurka ta yi ta matsin lamba ga gwamnatin ta Pakistan don ta saki Baradar ɗin wanda aka kame tun a cikin shekara ta 2010.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Abdourahamane Hassane