Pakistan ta yanke wa Shakil Afridi hukuncin dauri na shekaru 33
May 25, 2012A matsayin martaninta ga hukuncin dauri a gidan yari na shekaru 33 da aka yanke wa likitan da ya taimaka wajen gano mabuyar Bin Laden a kasar Pakistan, majalisar dattawan Amirka ta ce za ta rage tallafin kudin da ta ke bai wa kasar. Komitin kudin majalisar ya tsai da shawarar rage taimakon kudin daga dala miliyan dubu zuwa miliyan 33. Kenan kasar ta Pakistan za ta rinka samun dala miliyan daya a kowace shekara bisa hukuncin cin amanar kasa da aka yanke wa Shakil Afridi wanda ma'aikatar leken asirin Amirka CIA ta ba wa kwangilar gudanar da shirin allurar riga kafi a garin Abottabad domin gano kwayoyin halitta na jini da za su kai ga gano mabuyar bin Laden. 'Yan majalisar dattawan Amirka sun yi kira da a yi wa likitan afuwa a kuma sake shi ba da wani sharadi ba.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman