Masu cin zarafin mata zasu fara fuskantar hukunci a Pakistan
February 7, 2020Talla
Yayin amincewa da wannan bukata ministan harkokin majalisar dokokin kasar Muhammad Khan wanda ya gabatar da kudirin gaban 'yan majalisar, ya kara jaddada cewar kamata yayi masu irin wadannan laifuka su fuskanci rataya a gaban dandazon al'umma, kodayake ministar kare hakkin yan Adam Shireen Mazari ta bayyana cewar gwamnatin kasar bata da hannu a zabin wannan hukunci duk kuwa da yawaitar cin zarafin mata da kisan kananan yaran da ya zama ruwan dare a kasar.
A wani sabon labarin kuma Kungiyar kare hakkin yan Adam ta Amnesty International ta bayyana damuwa game da wannan mataki da Majalisar dokokin Pakistan din ta zaba, bayan jan hankali gwamnatin kasar ta kara daukar matakan kare yara da mata daga cin zarafi.