Paparoma na ziyara a Indonisiya
September 3, 2024Talla
A cikin kwanaki ukun da jagoran Kiristocin zai yi a Indonisiya, kasar da ke da mabiya addinan Islama miliyan 242, da suka ba ta damar zama kasa mafi yawan Musulmai a duniya, zai gana da shugaban kasa Joko Widodo daga bisa ni kuma ya yi huduba tasalama ga Kiristocin kasar kimanin miliyan takwas.
Dan shekaru 87- da ke fama da rashin lafiya, Paparoma Francis, zai yi kwana 12 yana ziyartar kasashe hudu domin wanzar da alaka mai kyau a tsakanin Kiristoci mabiya darikar Katolika da sauran addinai. Ana sa ran yaziyarci kasashen New Guinea da East Timor da kuma Singapore baya ga Indonisiya da yanzu ya fara da ita.