1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma na yin taron aduo'i na matasa a Panama

Abdourahamane Hassane
January 25, 2019

Jagoran darikar Roman Katolika Paparoma Francis zai kai ziyara a cikin wani gidan fursuna na masu karancin shekaru a Panama.

https://p.dw.com/p/3C9aO
Vatikan Papst Franziskus während der Generalaudienz
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/M. Valicchia

Paparoma Francis zai yi aduo'in a cikon kwanaki uku na wata haduwa ta matasa na duniya baki daya da za a ci gaba da yi har ya zuwa ranar Lahadi. Masu aiko da rahotannin sun ce Paparoma zai tattuana da fursunoni yara wadanda wasu suka aikata mayan laifuka domin yi musu huduba. Sama da matasa dubu 200 daga kasashe na duniya daban-daban za su halarci wadannan aduo'i da za a kankare bikin ranan Lahadi mai zuwa a Panamar da ke a yankin tsakiya na Amirka