1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma na ci-gaba da ziyararsa a Kwango

Mouhamadou Awal Balarabe
February 2, 2023

Paparoma Francis na maida hankali kan lamuran coci da ke taka muhimmiyar rawa a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango mai fama da tashe tashen hankula. Idan ya tashi kwango, zai je Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/4N0Go
Lokacin da Paparoma Francis ke karbar kyauta a Kinshasa na KwangoHoto: Arsene Mpiana/AFP

Ana sa ran shugaban mabiya darikar Katolika zai je filin wasa da ke birnin Kinshasa domin ganawa da matasan Kwango da ke zama kasa ta biyu da ta fi yawan 'yan Katolika a Afirka, kafin ya gabatar da jawabi a gaban kimanin mutane 80,000.

Wannan dai ita ce ziyara ta 40 da shugaban darikar Katolika ya gudanar tun bayan da aka zabe shi a shekara ta 2013, sannan karo na biyar a nahiyar Afirka. A gobe Jumma'a, Paparoma Francis zai je Juba babban birnin Sudan ta Kudu da ke zama 'yar autar kasashe kuma daya daga cikin mafiya talauci a duniya.