1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daidaito wajen rabon allurar Covid-19

December 25, 2020

Shugaban darikar katolika na duniya paparoma Francis ya yi kiran yin adalci da samar da daidaito wajen rabon allurar rigakafin corona ga kowa da kowa a duniya

https://p.dw.com/p/3nDxM
Vatikan Petersdom Papst Franziskus Segen "Urbi et orbi"
Hoto: Vatican Media/AP Photo/picture alliance

Kiristoci a fadin duniya sun gudanar da bukukuwan Kirsimeti inda miliyoyin jama'a suka takaita bukukuwan saboda annobar Corona.

A Jawabin da ya gabatar a fadrsa ta Vatican shugaban darikar Katolika na duniya Paparoma Francis ya bukaci samar da allurar rigakafin corona ga kowa, abin da ya baiyana da cewa shi ne kadai fatan da ya rage wa al'umma a wannan yanayi da ake ciki na rashin tabbas.

Paparoman ya kuma yi kira shugabannin kasashe da yan kasuwa da kuma kungiyoyin kasa da kasa su karfafa hadin kai da zumunta a tsakanin al'umma ba wai gogayya ba.

Ita ma a jawabinta na shekara shekara sarauniyar Ingila Elizabeth ya ta baiyana fatan samun sauki daga mawuyacin halin da duniya ta sami kanta a ciki.