1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Paparoma ya buƙaci samun masalaha a rikicin nukiliyar Iran

April 16, 2006
https://p.dw.com/p/Bv1n

Yayin da Kiristoci a duniya baki ɗaya, ke cigaba da bukukuwan Easter, Paparoma Benedict na 16, ya jagoranci adduói na musamman a dandalin St Peters dake birnin Rome. Dubban mahajjata da yan yawon buɗe idanu suka halarci taron adduoin. A jawabin sa ga alúmar duniya, Paparoma Benedict ya yi kira da a samo hanyoyi na masalaha domin warware taƙaddamar nukiliyar ƙasar Iran, da samar da yantacciyar ƙasar Palasɗinawa da kuma haɗa hannu a tsakanin kasashe, domin shawo kan ayyukan tarzoma a duniya. Ya kuma ambato yankuna da ake fama da rikici a nahiyar Afrika, inda ya bukaci sasantawa tare da gano bakin zaren warware waɗannan rikice rikice.