Paparoma ya nemi gafarar musulmin Bama
December 1, 2017Talla
Wannan ne karon farko da Paparoma Francis ya kira sunansu musulmin na Bama, wato 'yan Rohingya a ziyarar da yake yi a kasashen Myanmar da Bangaladash. Shugaban na mabiya akidar ta Katolika, ya ce ya roki gafarar ce a madadin wadanda suka wulakanta su da ma juya masu baya da wasu manyan kasashe suka yi yayin da suke cikin matsala.
Shi dai Paparoma ya ki ambaton sunan musulmin na Bama ne lokacin da yake a kasar Myanmar, inda Cocin Katolika dake kasar ta bukaci ya girmama ra'ayoyin al'umar kasar da ke da rinjaye. Ita dai al'umar ta Rohingya, na matsayin tsiraru ne a Myanmar.