Paparoma ya nuna damuwa kan rikicin Iran
January 9, 2020Firaminista Birtaniya Boris Johnson ya yi kira da a "kawo karshen tashin hankali" tsakanin Iran da Amirka, a lokacin da ya tattauna ta wayar tarho da shugaban Iran Hassan Rohani. Cikin sanarwa da Kakakinsa ya bayar a birnin Landan, Johnson da ke da ra'ayin mazan jiya ya bayyana ci gaba da aiki da yarjejeniyar makamashin nukiliyar Iran tare da musayar yawu don kauce wa yaduwar rikici.
Shi ma Paparoma Francis ya nuna damuwarsa a game da abin da ya kira hadarin yaduwar rikicin Amirka da Iran zuwa wasu kasashe na duniya. Shugaban darikar katolika ya yi kira da a kara himmatuwa a manyan kasashen duniya wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.
Tuni shugaban Amirka Donald Trump ya maida wukarsa cikin kube tun a ranar Laraba bayan da Iran ta harba makami mai linzami a kan sansanonin da sojojin Amirka nke tsugune a Iraki, a wata ramuwar gayya ga Washington bayan da ta halaka Janar Qassem Soleimani a birnin Baghadaza