Paris: Ana cigaba da farautar 'yan fashi
January 11, 2018Talla
Ya zuwa maraicen jiya Laraba, 'yan sanda sun ce sun kama mutum 3 da ake zargi da hannu a fashin kuma suna cigaba da neman karin wasu mutane da ake tunanin suna da hannu a fashin da aka yi a tsakiyar birnin na Paris.
Gidan talabijin din BFM da ke Faransa ya ce darajar kayan da aka sace ta kai sama da dalar Amirka miliyan 5 kuma ya zuwa yanzu ba a kai ga tantace ko 'yan sanda sun samu sukunin samo wasu daga cikin kayan da aka sace ba.
Birnin na Paris dai ya yi kaurin suna wajen aikata irin wadannan manyan laifuka da suka hada da sata da kuma fashi da makami.