Kokarin kawo karshen zanga-zanga a Paris
December 6, 2018A Faransa a dai dai lokacin da masu zanga-zangar nuna kyama da matakan harajin gwamnatin kasar na Gilets Jaunes ke shirin sake fantsama a kan titunan birnin Paris a ranar Asabar mai zuwa Shugaban kasar Emmanuel Macron ya bayyana fargabar sake fuskantar irin tashin hankali da aka gani a makon da ya gabata a lokacin gangamin.
A kan haka ne ma ya yi kira ga shugabannin siyasa da na kungiyoyin kwadago da su sanya kiran zaman lafiya da kiyaye jamhuriya domin a cewarsa halin da ake ciki a kasar a yanzu batu ne na makomar jamhuriya ba na wata adawa ba.
Yanzu haka dai duk da sassaucin da gwamnatin Faransar ta yi na dakatar da wasu matakan da suka haddasa zanga-zangar, kungiyoyi dabam-dabam da suka hada da na daliban makarantun Sikandare da na jami'o'i da kungiyoyin manoma na kasar sun yi kira ga magoya bayansu da su halarci zanga-zangar ta Gilets Jaunes a ranar Asabar mai zuwa.
A makon da ya gabata dai mutane hudu ne suka mutu wasu daruruwa suka ji rauni a lokacin zanga-zangar nuna adawa da matakan harajin kasar ta Faransa wacce ta rikide zuwa tarzoma.