1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Paris2024: An tsaurara tsaro wajen Olympics

July 26, 2024

An tsaurarar matakan tsaro a Faransa, yayin da ake kaddamar da gasar wasannin Olympics. Faransar dai na son bai wa duniya mamaki a kayataccen bikin da ke zuwa yayin da ake nuna fargabar tsaro da kuma dambarwar siyasa

https://p.dw.com/p/4inM7
Paris2024: Gasar wasannin Olympics
Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

Kimanin jami'an ‘yan sanda 45,000 ne tare da sojoji 10, 000 da ma wasu jami'an tsaron masu zaman kansu aka tsara cewa za su tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama'a a ciki da kewayen inda ake bikin kaddamar da gasar wasannin na Olympics na birnin Paris da ke ci a wannan rana.

Bayan gasar Olympics ta duniya da aka yi a Beijing na kasar China a 2022, manyan yake-yake biyu na Ukraine da na Zirin Gaza sun dauki hankalin duniya, matsalolin da aka hakikance cewa sun shafi hatta gasar ta wannan karo.

Paris2024: Tsaro a gasar Olympics
Paris2024: Tsaro a gasar OlympicsHoto: Andy Wong/AP/picture alliance

Yanzu dai Faransa na mataki na kololuwa ta fuskar tsaro, duk da yake jami'ai sun kore duk wata barazana musamman a wannan lokaci na kaddamar da gasar ta Olympics.

An kuma bayyana wasu mutum 155 a matsayin wadanda za a yi matukar sanya idanu a kansu tare da takaita musu zirga-zirga saboda dalilai masu nasaba da dokoki na ta'adda.

Shugaban kasar Senegal Basirou Diomaye Faye, wanda ke cikin shugabannin kasashe da suka halarci bude gasar, ya yi jawabin da ya tabo batun tsaro da kuma wariya da ake nuna wa wasu a wajen wasanni makamantan wannan.

"Burin wannan gasa ta Olympics dai ya gamu da kalubalen yaki da wasu nau'uka na rigingimu gami da karuwar rashin daidaito a tsakanin kasashe.  Wannan kuma wata dama ce ta jan hankalin wannan taro ga bukatar daukar mataki kan wariya da bambanci saboda launin fata da ake yawan yi lokacin wasanni musamman inda ake kalaman nuna kiyayya..

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel MacronHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Shugabannin kasashe 50 suka halarci taron da aka yi a birnin Paris gabanin kaddamar da gasar a wannan maraice.

A lokacin karbar manyan bakin gabanin kaddamar da gasar ta Olympics a hukumance, shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya jaddada matsayin hadin kan kasashe wajen cimma nasarar wasannin.

"Samun hadin kai cikin dukkanin abubuwan da za mu zama tare a kai a harkar wasannin nan, abu ne muhimmi a gare mu. Ina muku godiya da haduwar da duk muka yi a nan. Wasannin dai hanya ce ta haska abin da muke yi wajen kaddamar da burin da muka sanya a gaba. Ina mika godiya da samun taimakon kudade da aka samar wa kasashen Afirka da na Latin Amurka da ma kasashen yankin Pacific, sannan duk wani abu da aka yi wajen cimma hakan, su ma abin godiya ne a gare ni.”

'Yan sanda na sa ido kan tsaro wajen gasar Olympics
'Yan sanda na sa ido kan tsaro wajen gasar OlympicsHoto: Andrew Medichini/AP/picture alliance

A shekaru biyun da suka gabata ne dai Faransa ta yi nasarar samun damar daukar nauyin wannan gasa ta Olympics da take fatan za ta karfafa tarihin da gwamnatin Shugaba Emmanuel Macron za ta kafa.

Akalla dai ‘yan kallo mutum dubu 300 ne za su kasance wajen gasar da za ta hada ‘yan wasa daban-daban har 7, 500.

An kuma zuba 'yan sanda gwanayen harbi a wasu muhimman wurare da za su dauki hankali a bikin, abin da ake ganin yana da alaka da abin da ya faru a Amurka, na yunkurin kisan tsohon shugaban kasar Donald Trump da aka yi a ranar 13 ga wannan watan.