1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Peru ta kori jakadan Mexico

December 21, 2022

Kasar Peru ta kori jakadan Mexico daga kasarta. A cikin sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce ta bai wa Pablo Monroy wa'adin sana'o'i 72 da ya bar kasar.

https://p.dw.com/p/4LHkY
Peru Lima | Jami'an 'yan sanda a gaban offishin jakadancin Mexico
Hoto: Liz Tasa/REUTERS

Ma'aikatar ta ce an dauki wannan mataki ne sakamakon sanarwar da manyan hukumomin Mexico ke fitarwa kan dambarwar siyasar da ta kunno kai a Peru. A martanin da Mexico ta mayar, ta ce offishinta na Lima zai ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda ya saba, tare kuma bayar da umurnin mayar da jakadanta.

Da dama dai na ganin hakan baya rasa nasaba da sanarwar da Mexico ta fitar na bai wa hambararren shugaban kasar Peru Pedro Castilo mafaka a kasarta. An dai tsige shugaba Castilo ne da yanzu haka yake a tsare, biyo bayan tuhumar da ake masa da rashin da'a da ma yunkurin rusa gwamnati.