Ping na nema a shiga tsakaninsa da Bongo
June 2, 2017Madugun 'yan adawan Gabon Jean Ping ya bukaci kasashen duniya sua kawo masa dauki a kokarin da yake yi na darewa kan karagar mulki kasarsa ba tare da zubar da jini ba. A lokacin wani taron manaima labarai da ya gudanar da LIbreville, Ping ya jadadda cewar shi ne ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Agustan 2016, tare da zargin Ali Bongo Ondimba da murde wannan zabe.
Wannan sabuwar kiki_kaka na zuwa ne kwanaki kalilan bayan kammala taron sasantawa da ya gudana tsakanin bangaren da ke mulki da na adawan gabon, taron da Jean Ping ya ki halarci duk da kiraye-kirayen da aka yi masa.
Tashin hankali ne dai ya barke a Gabon a farkon watan Satumban bara bayan da aka sanar da Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya samu damar yin tazarce a wannan karamar kasa mai al'umma miliyan daya da dubu 800. A shekara ta 2009 ne dai aka zabi Ali Bongo a matsayin shugaban kasar Gabon bayan rasuwar mahaifinsa Omar Bongo.