Masu shugar da kara sun wanke Platini
May 26, 2018Talla
Kiran ya biyo bayan sanarwar data fito daga wajen masu shigar da kara na kasar Switzerland a wannan Asabar, da ke nuni da cewar, babu wata shaida data tabbatar da zargin da ake wa Platini.
Lauyan da ke kareshi Vincent Solari, ya ce a yanzu haka an wanke tsohon shugaban hukumar wasan kwallon kafar Turan, don haka babu wata shari'a a kansa. Sai dai ofishin masu shugar da karar da ke Switzerland, ya nunar da cewar, za'a cigaba da gudanar da bincike a kan Platini.
A shekara ta 2015 nedai hukumar FIFA ta dakatar da Michel Platini daga shiga duk harkokin wasan kwallon kafa har na tsawon shekaru takwas, ka na daga bisani ta rage zuwa hudu, dangane da bakadalar dalar Amurka miliyan biyu da ya karba daga hukumar FIFa a 2011.