1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Pompeo: Ziyarar karfafa kawance da Jamus

Abdullahi Tanko Bala
June 1, 2019

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompea ya gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin a ziyarar wasu kasashen Turai.

https://p.dw.com/p/3JanT
Deutschland Berlin | US Außenminister Mike Pompeo auf Staatsbesuch mi Angela Merkel
Hoto: Reuters/F. Bensch

Ziyarar ta zo a lokacin da dangantaka ta yi rauni tsakanin Amirka da Jamus sakamakon matakin Trump ya kebance kansa daga dangi.

Mikel da Pompeo sun yi ganawa ta tsawon mintuna 45 inda suka tattauna batutuwa da dama da suka hada da wadandan kasashensu biyu suke da sabanin ra’ayi da kuma wadanda ra’ayinsu ya zo daya.

Bayan ganawar Pompeo ya baiyana Jamus da cewa aminiya ce ta kwarai. Yace kasashen biyu za su aiki tukuru wajen cimma nasara kan tsaro da zaman lafiya.

Ita ma a nata bangaren Merkel ta ce Amirka z ata cigaba da zama babbar kawa ga Jamus

"Wannan ziyara ta nuna tsawon shekaru da muka yi muna kawance da juna, wanda muke bukata a yanzu fiye da kowane lokaci a baya a wannan karni na 21. Amirka za ta cigaba da kasancewa babbar abokiyar kawancen Jamus a wajen nahiyar Turai".