1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniTurai

Potugal ta sha da kyar a hannun Chek a gasar Euro 2024

Mouhamadou Awal Balarabe
June 19, 2024

A ci-gaba da wasannin rukuni na neman lashe gasar kwallon kafa ta kasashen Turai da ke gudana a Jamus, Turkiyya ta samu nasara a kan Jojiya a birnin Dortmund, yayin da Potugal ta doke Jamhuriyar Czech a birnin Leipzig.

https://p.dw.com/p/4hFP0
'Yan wasan Potugal sun yi gwagwarmaya wajen doke Jamhuriyar Chek
'Yan wasan Potugal sun yi gwagwarmaya wajen doke Jamhuriyar ChekHoto: Sunday Alamba/AP Photo/picture alliance

Duk da cewa Jamhuriyar Chek na bin su kwallo da Lukáš Provod ya ci a minti na 62 da fara wasa, amma Cristiano Ronaldo da takwarorinsa na Potugal ba su firgita ba, inda suka ci gaba da mayar da hankali kan burinsu na samun nasara. Hasali ma Kokarin na 'yan Potugal ya biya mintuna bakwai bayan haka, inda darar da Robin Hranáč ya saba ta ci gida ta hanyar zuwa kwallo a gidansu. Sannan daga karshe, Potugal ta samu nasara biyo bayan kwallon da Francisco Conceição ya ci bayan karin lokaci.

A Takaice, an tashi wasan Seleção ta Potugal na da ci biyu yayin da Jamhuriyar Chek ke da daya, lamarin da dadada ran  koci Roberto Martinez wanda ya ce: "Abin da ya fi burge ni shi ne da'ar 'yan wsa. A daidai lokacin da ake gabanmu da 1-0, mun samu damar sarrafa wasa yadda ya kamata. Zai iya kasancewa abu mai sauki mu zargin juna, amma ba mu yi hakan ba. Mun zama tsintsiya madaurinki daya. Ina ganin cewar abu ne mai muhimmanci mu rika jerawa tare, kuma mu ci gaba da amfani da 'yan wasa da muke da su a cikin tawagarmu."

 Cristiano Ronaldo ya taimaka wajen ceto Potugal daga hannun 'yan wasan Chek
Cristiano Ronaldo ya taimaka wajen ceto Potugal daga hannun 'yan wasan ChekHoto: Petr Josek/AP/picture alliance

Wannan nasarar da ta samu ta sanya Potugal a matsayi na biyu a rukunin H, bayan Turkiyya wacce da ci 3-1 ta lallasa 'yar auta Jojiya da ta yi wasanta na farko a gasar Euro a birnin Dortmund. Dimbin 'yan asalin Turkiyya da ke da zama a Jamus sun shafe dare suna wake-wake da raye-raye don murnar nasarar da kasarsu ta samu.

Jamus na kalubalantar Hangari a wasanta na biyu

A wannan Alhamis 19.06.2024 ne ake gudanar da wasannin rana ta biyu ta wasannin rukuni, kuma wasan da zai fi daukar hankali a rukunin A shi ne karawa da Jamus mai masaukin baki ke yi da Hangari. Hasali ma, kocin Mannshaft Julian Nagelsmann ya bayyana aniyar amfani da 'yan wasa 11 da suka doke Scotland da ci 5-1.

Daya daga cikin 'yan wasan Jamus Maximilian Mittelstädt ya ce zai kasance abu mai mahimmanci sun yi amfani da dabarun da suka yi amfani da su a wasan farko. Ya ce: "Muna so mu sake buga salon wasa iri wanda muka yi a karawa da Scotland. Idan ba mu ba yi tsayuwar daka ba, za a iya hukunta mu saboda Hangari na da dan wasa mai karfi mai suna Szoboszlai, wanda zai iya zama mai hatsarin gaske a cikin kankanin lokaci. Mune ya kamata mu yi taka tsantsan."

Doke Scotland da Mannschaft ta Jamus ta yi zai iya tasiri a wasanni na gaba
Doke Scotland da Mannschaft ta Jamus ta yi zai iya tasiri a wasanni na gabaHoto: Andrew Milligan/empics/picture alliance

A nata bangaren, Scotland da ke da kishin daukar fansa bayan shan kaye a hannun Jamus za ta kalubalanci Switzerland a birnin Cologne. Amma Switzerland za ta so ci gaba da karyawa inda ba gaba bayan doke Hangari da ta yi da ci 3-1 a wasan farko. Sai dai mai tsaron baya Manuel Akanji na kaffa-kaffa game da Scotland, inda ya ce: "Scotland ta yi rashin nasara a wasanta na farko, amma ba na jin cewar 'yan wasanta sun nuna duk basirarsu. Amma mu ma, muna son samun wannan maki ukun don cimma burinmu. Dole ne mu kasance cikin shiri tun farkon wasan kuma mu sake yin wasa mai kyau."

Kuroshiya da Albaniya na gwanda kwanji

A rukunin B, Albaniya na kalubalantari Kuroshiya a birnin Hamburg. Dama, tawagar Kuroshiya na cikin mummunan hali bayan da ta sha kashi a hannun Spain a wasan farko duk da kaiwa matakin kusa da na karshe da ta yi a gasar cin kofin duniya na kwallon kafa da ta gabata. Tabbas 'yan kasar Kurushiya na dogara kan tauraronsu Luka Modric,  amma  Albaniya ta saba fita daga tarkon da abokan hamayya ke dana mata, inda ta tabbatar da hakan a karawa da ta yi da Italiya ta hanyar cin kwallo a cikin dakika 22 da fara wasa karkashin dan wasan Emir Bajrami, kwallon da ke zama mafi sauri a tarihin gasar kwallon kafa ta Euro.