Puigdemont: Zan zauna Belgium domin tsaro
October 31, 2017Shugaban yankin Kataloniya da aka kora Carles Puigdemont wanda kuma ke fuskantar tuhumar cin amanar kasa a Spain bisa jagorantar ayyana ballewar yankin, wanda a yanzu haka yake Belgium yace ba wai ya je kasar bane domin guduwa ko neman mafakar siyasa ba.
Bai dai baiyana zuwa tsawon wani lokaci ne zai zauna a kasar ta Belgium ba, sai dai ya ce zai koma ne kawai idan gwamnatin Spain ta bashi tabbacin samun adalci.
Carles Puigdemont ya shaidawa manema labarai a Brussels cewa ya amince da zaben da mahukunta a Spain suka bukaci a gudanar a Kataloniya.
Tun da farko ministan harkokin wajen Spain yace zai yi mamaki idan Belgium ta baiwa Puigdemont mafakar siyasa.
Babban lauyan gwamnatin Spain dai ya gabatar da tuhumar laifuka da suka hada da cin amanar kasa kan Puigdemont laifin da ka iya daukar hukuncin shekaru 30 a gidan yari idan kotu ta tabbatar da shi.