Putin na nazarin kaurace wa taron G20
November 10, 2022Ofishin jakadancin Rasha da ke Indonisiya ne ya sanar wa da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, haka a Alhamis din nan. A maimakon hakan, ofishin jakadancin ya ce ana sa ran Shugaba Putin zai halarci taron ta hanyar bidiyo.
Da ma dai tun kafin yanzu shugaban Amirka Joe Biden ya lashi takobin ba zai kula Shugaba Putin ba idan sun hadu a taron G20 a sakamakon yadda Rasha ke kaddamar da yakin da ke hallaka mutane a kasar Ukraine. Sai dai kuma wasu bayanai na nuni da cewa shugaban na Rasha ba zai halarci taron ba kwata-kwata, inda ya shirya tura ministansa na harkokin kasashen waje domin ya wakilci Rasha a taron.
A watan Yulin da ya gabata, ministan harkokin wajen Rasha ya fice daga taron ministocin kasashen G20 din bayan da taron ya baje laifukan da Rasha ke aikata wa a Ukraine.