1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin da Erdogan sun tattauna kan Siriya

Abdullahi Tanko Bala
March 5, 2020

Halin da ake ciki a Idlib ya yi tsanani wanda ya sa shugabannin Rasha da Turkiyya ganin dacewar tattaunawa gaba da gaba don samo masalaha.

https://p.dw.com/p/3YujQ
Russland Moskau | Recep Tayyip Erdogan und Vladimir Putin
Hoto: picture-alliance/AA/M. Cetinmuhurdar

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a birnin Moscow a wannan Alhamis da nufin kawo karshen fada a arewa maso yammacin Siriya wanda ya hada da sojojinsu, lamarin da ya gwara kan kasashen biyu.

Gabanin ganawar ta baya bayan nan shugaban rasha Vladimir Putin da shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan sun yi kokarin daidaita muradunsu a Siriya duk da cewa Moscow na goyon bayan shugaban Siriya Baashar al Assad yayin da Turkiyya ke maraya wa 'yan tawaye baya a yakin da aka kwashe shekaru tara ana gwabzawa. 

A halin da ake ciki kasashen biyu Rasha da Turkiyya sun nuna zakuwa ta kaucewa fito na fito sai dai sabani kan muradun da kowannensu ke da shi a lardin Idlib ya sa an kasa cimma masalaha a tsakaninsu wadda kowa zai aminta da ita.

Rasha ta taimaka wa Siriya kwace iko da yankin Idlib da ke zama tungar karshe ta 'yan tawaye, yayin da a waje guda Turkiyya ta tura dubban sojojinta zuwa yankin na Idlib domin fatattakar sojojin Siriya.