1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin da Erdogan sun zanta kan Libiya

Ahmed Salisu
August 17, 2020

Shugaba Vladmir Putin na kasar Rasha ya yi wata tattaunawa ta wayar tarho a yau da takwaransa na Turkiyya Recep Tayyib Erdogan kan rikicin da ke cigaba da wakana a kasashen Libiya da Siriya.

https://p.dw.com/p/3h5WV
Russland Moskau | Recep Tayyip Erdogan und Vladimir Putin
Hoto: Imago Images/ITAR-TASS/M. Metzel

Fadar mulkin Rasha ta Kremlin ta ce shugabannin biyu sun fi bada karfinsu ne kan Libiya inda suka jaddada goyon bayansu ga bangaren adawa sannan suka bayyana bukatar da ke akwai kan a yi dukannin mai yuwuwa wajen cimma yarjejeniya ta tsagaita wuta a rikicin kasar.

Dangane da batun Siriya kuwa, Putin da Erdogan sun amince da samar da wata runduna da za ta yaki ta'addanci a kasar ta Siriya bayan da aka farwa wata rundunar ta hadin gwiwa ta Turkiya da Rasha da ke sintiri a yankin nan na Idlib.

Baya ga batun na Siriya, fadar mulkin Shugaba Erdogan ta kuma ce shugaban da na Rasha sun kuma magantu kan rikicin Turkiyya da Girka wanda ke da nasaba da makashi a gabashin Tekun Bahar Rum, inda suka amince kan cigaba da tattaunawa don samo bakin zaren warware matsalar.