Putin na neman hanyar waware rikicin Iran
August 14, 2020Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci da a gudanar da taron koli na kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus da Iran, don gano bakin zaren warware takaddamar nukiliyar Iran. Wannan sanarwar ta zo ne a yayin da Amirka ta kuduri aniyar tsawaita takunkumin kan cinikin makamai da Teheran, wanda ya kamata ya kare a ranar 18 ga Oktoba. Sai dai Rasha ta ki ba da kai a kan wannan batu saboda a cewar ta, zai maida hannu agogo baya a kokarin sulhunta rikicin na Iran.
Shugaban na Rasha ya ce lokaci ya yi da za a nemi kauce wa duk wani rikici da zai ci gaba da jefa tattalin arzikin Iran cikin mawuyacin hali. Kasar Amirka wacce ta janye daga yarjejeniyar nikiliyar Iran a watan Mayun 2018, tana neman ci gaba da ja wa Iran birki a fannin siyan makamai. Sai dai kasashen China da Rasha, wadanda ke da kujerar na ki a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suna adawa da matakain tsawaita wannan takunkumin.