Rasha na tattaunawa da kasashen Turai
October 2, 2015Kasar Rasha ta bayyana cewa ta yi lugudan wuta kan wata cibiyar mayakan IS a birnin Raqa na kasar Siriya a daidai lokacin da shugaba Putin na kasar ta Rasha ke ganawa da shugabannin kasashen Faransa da Jamus da Ukraine inda ake ganin tattaunawar tasu za ta maida hankali kan kutsen Rasha a Ukraine, yayin da a bangare guda kuma ake tunanin abin da kasar ta Rasha ke son cimmawa a Siriya.
Kasashen Yamma dai na kallon Rasha a matsayin wacce ba batun murkushe mayakan na IS ne ke gabanta ba illa fafutika wajen ganin ta bada kariya ga jagorancin shugaba Assad tshohon aboki a garesu.
A ranar Juma'an nan kawancen sojan da ke samun jagorancin Amirka sun yi gargadi ga dakarun na Rasha cewa su yi taka tsatsan wajen kauce wa dakarun soja da ke adawa da gwamnatin ta Siriya inda a bangaren kasashen Turkiya da Saudiyya da Amirka kuma ke neman ganin Rashar ta tsaida farmakin da take zargin tana kaiwa kan 'yan adawa da fararen hula.