1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Putin zai ziyararci Koriya ta Arewa

Suleiman Babayo
June 17, 2024

Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai kai ziyarar nuna "abota" zuwa Koriya ta Arewa inda zai gana da jiga-jigan kasar da yake smaun makamai kan yakin da yake yi da kasar Ukraine.

https://p.dw.com/p/4h94g
Rasha | Kim Jong Un und Vladimir Putin a Kosmodrom Wostotschny
Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa da Shugaba Vladimir Putin na RashaHoto: Yonhap/picture alliance

A gobe Talata, ake sa ran Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai kai ziyarar nuna abota kasar Koriya ta Arewa kamar yadda fadar mulkin kasar ta Kremlin ta tabbatar, domin nuna godiya da samun makamai daga mahukuntan Koriya ta Arewa a yakin da ke faruwa bayan Rasha ta kaddamar da kutse kan kasar Ukraine.

Wannan ziyara ta Putin tana zuwa lokacin da yake kara neman makamai tare da zama saniyar ware tsakanin kasashen duniya, tun bayan kutsen da ya kaddamar kan Ukraine a watan Fabarairun shekara ta 2022. Mahukuntan na Rasha sun ce bayan ziyarar kwanaki a Koriya ta Arewa daga bisa Shugaba Vladimir Putin na kasar ta Rasha zai wuce zuwa kasar Vietnam.