1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin da Erdogan za su gana kan Idlib

Yusuf Bala Nayaya
September 17, 2018

A wannan Litinin ake sa rai Shugaba Vladimir Putin na Rasha zai karbi bakuncin takwaransa na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan inda ake sa rai za su tattauna batun samar da zaman lafiya a yankin Idlib na Siriya.

https://p.dw.com/p/34ycn
Teheran Treffen Putin Erdogan
Putin da Erdogan a tattaunawar makon jiya a IranHoto: picture-alliance/AA/R. Aydogan

Tattaunawar dai za a yi ta ne a birnin Sochi na kasar ta Rasha, zaman shugabannin da ake ganin ci gaba ne kan tattaunawar da aka faro a makon jiya da kasar Iran ta dauki nauyi inda a makon Putin ya noke ga batun tsagaita bude wuta baki daya a kasar ta Siriya.

Kawo yanzu dai Rasha wacce ke zama babbar mai goyon bayan dakarun Siriya ta amince a zame 'yan ta'adda daga cikin batun tsagaita wuta kan lugudan wutar da Turkiyya ke neman ganin an yi.

Turkiyya dai na nuna fargabar fantsamar karin dubban 'yan gudun hijira zuwa kasarta muddin aka ci gaba da barin wuta a birnin na Idlib wanda ba shi da nisa da iyakar kasar.