1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin zai shiga tsakani a rikicin Ukraine

August 31, 2014

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi kira da a fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan awaren da ke goyon bayan kasarsa, amma a yi batun yiwuwar sabon yanki.

https://p.dw.com/p/1D4UL
Wladimir Putin
Hoto: S.Chirikov/AFP/Getty Images

A wannan lahadin, shugaba Vladimir Putin na Rasha ya yi kira da a fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Ukraine da 'yan awaren da ke goyon bayan Rasha, inda ya yi kira da a tattauna har da batun yiwuar girka sabuwar kasa. Putin ya ce akwai bukatar kaddamar da tattaunawa, kuma ba a kan abubuwan da ba a fayyace suke ba, a a, a duba tsarin siyasar kasar da yanayin al'ummar, a kuma yi la'akari da yiwuwar ballewar yankin kudu maso gabashin kasar.

Inda ya kara da cewa, burin shi ne, kare manufofin mutanen da ke yankin gabashin Ukraine

Wannan jawabi na Putin na zuwa ne wuni guda bayan da shugabannin Turai suka yi kira da ya jagoranci shirin sulhunta rikicin bangarorin na Ukraine, suka kuma yi barazanar daukan karin matakai idan har bai yi haka ba.

Kungiyar kawancen tsaron NATO, ta yi imanin cewa akwai akalla sojojin Rasha dubu daya, wadanda ke yaki tare da 'yan aware, abin da ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya karyata ya kuma kira shi zargin da ba shi da tushe.

Mawallafiya: Pinado Abdu Waba
Edita: Umaru Aliyu